Informações:
Sinopse
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episódios
-
Dakta Isa Abdullahi kan matakin CBN game da cire kudi a bankuna
04/12/2025 Duração: 03minBabban Bankin Najeriya ya sanar da cire shingen kuɗaɗen da jama'a ke ajiyewa a bankuna da kuma ƙara yawan kuɗin da ake ɗauka a bankin. Bankin ya ce daga yanzu an ƙara yawan kuɗin da mutum ka iya cirewa daga naira 100,000 zuwa naira 500,000, yayin da bankin ya ci gaba da riƙe naira N100,000 a matsayin kuɗin da mutum guda ka iya cirewa a ATM a rana guda. Domin duba tasirin wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki Dakta Isa Abdullahi, na Jami'ar Kashere, da ke jihar Gombe a Najeriya. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Janar Sani Kukasheka kan kalubalen tsaron da ke gaban Christopher Musa
03/12/2025 Duração: 03minShugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da sunan Janar Christopher Musa mai ritaya ga majalisar Dattawa domin amincewar ta ya zama ministan tsaro. Christopher Musa ya yi aiki a matsayin babban hafsan tsaron Najeriya daga ranar 23 ga watan Yunin 2023 zuwa 30 ga watan Octoban 2025, lokacin da shugaban ƙasar Bola Ahmad Tinubu ya yi masa ritaya. Idan majalisa ta amince, Janar Musa zai maye gurbin Badaru Abubakar da ya yi murabus a ranar Litinin. Bayanai sun nuna cewa fannonin da Musa ya fi ƙwarewa a kai shine fatattarkar ƴan ta’adda, da dubarun yaƙi, kasancewar ya yi aiki a matsayin jagoran rundunar sojojin Najeriya da ke kula da tsaron iyakokin Najeriya ta arewa maso gabashi da kuma yankin tafkin Chadi, haka nan ya kuma yi aiki a matsayin guda daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Sierra Leone, da kuma wasu ayyukan a Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya.. Domin sanin tasirin wannan nadin da kuma kalubalen dake gaban Janar Musa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon kakakin run
-
Yadda aka tarawa Najeriya dala miliyan 30 domin samar da tsaro a makarantu
03/12/2025 Duração: 03minƳan Najeriya na ci gaba da neman bayani a kan yadda wasu kuɗaɗen da aka tara, da yawan su ya kai dala miliyan 30 domin samar da tsaro a makarantu suka shiga, sakamakon sake dawowar satar ɗalibai a yankin arewacin ƙasar. A ƙarƙashin wannan shirin da ya fara a shekarar 2014, kasashe da dama suka tallafawa Najeriya, cikin su har da ƙasar Norway da ta bada dala miliyan guda, da wata dala miliyan guda daga Bankin Raya ƙasashen Afirka na AfDB, sai kuma Fam miliyan guda daga gwamnatin Birtaniya. Gwamnatin Switzerland ta bada taimakon dala miliyan takwas, yayin da Amurka ta bada dala miliyan biyu, sai kuma Qatar da ta bada dala miliyan biyu, yayin da ƴan kasuwan Najeriya su kuma suka bada taimakon dala miliyan 10. Ganin yadda aka kasa samar da tsaron a makarantu, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abubakar sadiq Umar Gombe. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Dakta Nasir Sani Gwarzo akan ranar HIV ta duniya
01/12/2025 Duração: 03minKamar dai kowace shekara, 1 ga watan Disamba ita ce ranar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta keɓe don yaƙi da cuta mai karya garkuwar jikin ɗan Adam wato HIV ko kuma SIDA. Bikin na bana ya zo ne a cikin wani yanayi da shugaba Donald Trump ya katse tallafin da Amurka ke bai wa ƙasashe masu tasowa ciki har da na ɓangaren yaƙi da wannan cuta. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Nasir Sani Gwarzo ƙwararren likitan yaƙi da annoba a Najeriya, wanda ya fara da bayyana halin da ake ciki game da yaƙi da HIV a ƙasar. Ga zantawarsu.
-
Kanal Sani Makiga kan ɗaukar sabbin ƴansanda dubu 50,000 a Najeriya
28/11/2025 Duração: 03minA tsakiyar wannan mako, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shelanta kafa dokar ta ɓaci kan sha’anin tsaro a faɗin ƙasar, matakin da a ƙarƙashi ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin jami’an Ƴansanda dubu 50,000 domin murƙushe matsalolin tsaron da ke ta’azzara. Kan wannan, da wasu ƙarin matakai da ake shirin ɗauka a ƙarƙashin dokar ta ɓacin kan tsaro Nura Ado Suleiman ya tattauna da Kanal Muhd Sani Makiga mai ritaya, masanin tsaro a Tarayyar Najeriyar. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...
-
Farfesa Tukur Abdulƙadir akan juyin mulkin Guinea Bissau
27/11/2025 Duração: 03minA jiya ne sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Umaro Sissiko Embalo, sakamakon rikicin zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a ƙarshen mako, a daidai lokacin da ake shirin gabatar da sakamako yau Alhamis. Shugaban da madugun yan adawa duk sun yi iƙrarin nasara, a kasar da ta yi ƙaurin suna wajen juyin mulki. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir dangane da juyin mulkin, wanda shi ne na biyar a kasashen Afirka ta Yamma, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai.
-
Farfesa Bello Bada kan matakan rufe makarantu saboda dalilan tsaro a Najeriya
26/11/2025 Duração: 03minGwamnatocin wasu jihohin dake arewacin Najeriya sun sanar da matakan rufe makarantun firamare da sakandare, wasu ma harda jami'oi, domin kaucewa matsalar garkuwa da daliban da ake samu, wanda ya kara ta'azzara a kasar. Domin duba tasirin matakin da kuma halin da yankin ya samu kan sa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokoto. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Malam Ahmad Abdurrahaman kan ɗaukar sabbin ƴansanda dubu 30 a Najeriya
25/11/2025 Duração: 03minShugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin ɗaukar sabbin ƴansanda dubu 30 da kuma janye masu gadin manyan mutane ba bisa ƙa'ida ba. Domin sanin tasirin wannan mataki da kuma yadda zai taimaka wajen inganta tsaro a ƙasar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon mataimakin Sifeto Janar na Ƴansandan Najeriya Malam Ahmad Abdurrahaman. Ku latsa alamar sauti donjin yadda zantawarsu ta gudana.............
-
Janar Sani Usman Kukasheƙa mai ritaya kan matsalar tsaro a Najeriya
24/11/2025 Duração: 03minA Najeriya, ƴan bindiga masu gurkuwa da mutane domin ƙarbar ƙudin fansa, sun tsanata kai hare-hare makarantu tare da sace ɗaibai a baya-bayan nan, lamarin da ya sa gwamnatoci a wasu jihohin ƙasar suka ɗauki matakin rufe makarantu a matakai daban-daban. Hakan ya biyo bayan sace dalibai a jihohin Kebbi da Neja a makon da ya gabata, lamarin da ya sake haifar da fargaba kan tsaron dalibai da makarantu da kuma makomar ilimi a yankin arewacin Najeriya. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunar Khamis Saleh da tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Sani Usaman Kukasheƙa mai ritaya..........
-
Amnesty ta zargi Chadi da gazawa wajen ɗaukar matakan kare mutanen da ake cin zarafin su
21/11/2025 Duração: 03minƘungiyar Amnesty International ta zargi hukumomin ƙasar Chadi da gazawa wajen ɗaukar matakan kare mutanen da ake cin zarafin su, sakamakon rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙasar, yayin da ta ce tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024, an kashe mutane 98, baya ga jikkata sama da 100 da kuma tilastawa ɗaruruwan iyalai barin muhallin su. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Isa Sanusi Daraktan kungiyar a Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai.
-
Dr Yahuza Getso kan sabbin hare-hare ƴan bindiga a Arewacin Najeriya
20/11/2025 Duração: 03minMatsalolin tsaro na ci gaba da ɗaukar sabon salo a Tarayyar Najeriya, bayan da a baya-bayan nan aka ga yadda ƴan bindiga a yankin arewa maso yammacin ƙasar suka sace ɗalibai aƙalla 25 a jihar Kebbi, yayinda ana tsaka da jimamin wannan kuma aka sake ganin yadda suka kai hari wata majami’ar jihar Kwara tare da kashe mutane 2 da kuma sace wasu da dama. Wannan na zuwa ne kwanaki bayan dakarun Sojin Najeriyar sun sanar da samun gagarumar nasara a kan ƴan ta’adda musamman bayan barazanar Trump ta ɗaukar matakin Soji kan ƙasar ta yammacin Afrika. Dangane da wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da masanin tsaro a Najeriyar Dr Yahuza Getso........
-
Kanal Muhammad Sani Makiga kan yadda matsalar tsaro ke komawa ɗanya a arewacin Najeriya
19/11/2025 Duração: 03minGwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya buƙaci rundunonin sojin Najeriya na sama da na ƙasa da kuma na ruwa, da su ƙaddamar da gagarumin farmaki kan sansanonin ƴan ta’addan da ke zagayen Yankin Tafkin Chadi, domin murƙushe matsalar tsaron da ta addabi Yankin. Kiran da gwamnan na Borno ya yi a farkon makon nan, na zuwa ne a yayin da matsalolin tsaro ke sake ta’azzara a sassan arewacin ƙasar, ciki har da satar ɗaliban da aka yi jihar Kebbi. Domin jin yadda masana tsaro ke kallon wannan lamari Nura Ado Suleiman ya tattauna da Kanal Muhammad Sani Ibrahim Makiga mai ritaya, masanin tsaro a Najeriya.
-
Hon Sani Ahmad Toro kan yadda Najeriya ta gaza samun tikitin World Cup
18/11/2025 Duração: 03minFatan Najeriya na samun gurbi a gasar cin kofin duniyar da za'a yi a shekara mai zuwa ya gushe, sakamakon rashin nasarar da ƙungiyar Super Eagles ta yi a hannun ƙasar Congo. Wannan shi ne karo na biyu a jere da Najeriya ba zata je gasar ta dunitya ba, bayan gaza zuwa Qatar shekaru 4 da suka gabata, kafin wannan karo. Bashir Ibrahim Idris, ya tattauna da tsohon sakatare janar na Hukumar Kwallon Kafa Najeriya, Hon Sani Ahmad Toro game da wannan koma baya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.
-
Sanata Bala Mohammad kan zaɓen sabbin shugabannin jam'iyar PDP a matakin ƙasa
17/11/2025 Duração: 03minBabbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP ta gudanar da babban taronta na ƙasa a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke yankin Kudu maso yammacin ƙasar, inda ta zaɓi sabbin shugabanninta a matakin ƙasa. Jam’iyyar ta ɗauki tsauraran matakai yayin taron mai cike da cece-kuce, ciki harda korar wasu manyan jiga-jiganta da suka haɗa da ministan Abuja Nyesom Wike da wasu ƙarin mutum 10. A tataunawarsa da Ahmad Abba, gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban gwamnonin PDP, Sanata Abdulkadir Bala Mohammad, ya ce umurnin kotu suka bi wajen gudanar da wannan taro kuma sun samu nasara. Ku latsa alamar sauti don sauraron zantawar tasu............
-
Hon Hamisu Mu'azu Shira kan dambarwar da ke tattare da babban taron jam'iyyar PDP
14/11/2025 Duração: 03minShugaban kwamitin shirya babban taron Jam'iyyar PDP na ƙasa a birnin Ibadan dake Najeriya, Umar Fintiri, wanda shi ne Gwamnan Adamawa, ya ce babu abinda zai hana su gudanar da taron da suka shirya gobe asabar. Fintiri ya bayyana haka ne bayan wani gagarumin taron da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da suka gudanar yau a birnin Abuja. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon Hamisu Mu’azu Shira, ɗaya daga cikin jiga jigan jam’iyyar, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.
-
Dr Harbau kan asarar kasuwar hannayen jarin Najeriya mafi muni a shekaru 10
13/11/2025 Duração: 03minKasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya ta tafka hasarar Naira Tiriliyan 4 da Biliyan 600 a ranar Talata, sakamakon matakin da masu linƙaya cikin kasuwar suka ɗauka na sayar da hannayen jarinsu cikin gaggawa saboda dalilai da dama ciki har da tsoron faɗuwa. Hasarar ta fiye da Naira Tiriliyan 4, ita ce mafi muni da kasuwar hannayen jarin Najeriyar ta fuskanta cikin shekaru 10. Domin jin dalilan da suka janyo aukuwar hakan da sauran lamura masu alaƙa, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Aminu Idris Harbau masanin tattalin arziƙi a Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar...
-
Ba mu taɓa bai wa wani ɗan ta’adda ko anini ba – Malam Uba Sani
12/11/2025 Duração: 03minDai dai lokacin da wasu jita-jita ke nuna cewa mahukuntan Najeriya kan biya kuɗaɗen fansa ga ƴan bindiga gabanin kuɓutar da ɗimbin mutanen da suke garkuwa dasu, ko kuma ga waɗanda suka aje makamansu a jihohin arewa maso yammacin ƙasar, Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi iƙirarin cewa bai taɓa biyan ko sisin kwabo ga ƴan bindiga ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Gwamna Uba Sani da Khamis Saleh................
-
Abubakar Ibrahim kan taron sauyin yanayi na COP30 da ke gudana a Brazil
11/11/2025 Duração: 03minAn bude traon Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi da ake kira COP 30 a Brazil inda masana muhalli da sauyin yanayi daga kasashen duniya da kuma kungiyoyin kare muhallin ke halarta a kasar Brazil. Za'a kwashe makwanni biyu ana gudanar da wannan taro wanda zai mayar da hankali a kan ci gaba ko akasin haka da aka samu a kan wannan matsala. Dakta Abubakar Ibrahim, Malami kuma mai bincike a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria ya yi tsokaci a kan matsalar musamman ganin irin illar da take yi a yankin arewacin Najeriya. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawarsa da Bashir Ibrahim Idris.
-
Gwamnatin Yobe za ta gina sabon asibitin ƙoda a Gashua inda cutar tafi ƙamari
10/11/2025 Duração: 03minGwamnatin Jihar Yobe dake Najeriya tace za ta ƙara gina manya asibitoci a kananan Hukumomi 3 wadda suka hada da Gashua, Potiskum da kuma Nguru, baya ga gina wani wannan sabon asibitin kula da masu fama da cutar ƙoda a Garin Gashua inda cutar tafi ƙamari a jihar. Haka kuma gwamnatin ta ce zata gina wasu makarantu na musamman a kowacce mazaɓa 178 da ake da su a jihar domin ƙara inganta karatun tun daga tushe. Gwamna Jihar, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da wakilinmu Bilyaminu Yusuf. Latsa alamar sauti don jin tattaunawarsu....
-
Barr Abdullahi Jalo kan ƙoƙarin warware barazanar Trump na kai hari Najeriya
06/11/2025 Duração: 03minYayin da ake ci gaba da lalubo hanyar warware matsalar barazanar Donald Trump na kai hari Najeriya, wasu masana na bayyana cewar ta hanyar diflomasiya kawai za a iya warware wannan dambarwa. Barr Abdullahi Ibrahim Jalo na ɗaya daga cikin su. Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda tattaunawar su da Bashir Ibrahim Idris ta gudana..............