Bakonmu A Yau

Kanal Sani Makiga kan ɗaukar sabbin ƴansanda dubu 50,000 a Najeriya

Informações:

Sinopse

A tsakiyar wannan mako, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shelanta kafa dokar ta ɓaci kan sha’anin tsaro a faɗin ƙasar, matakin da a ƙarƙashi ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin jami’an Ƴansanda dubu 50,000 domin murƙushe matsalolin tsaron da ke ta’azzara. Kan wannan, da wasu ƙarin matakai da ake shirin ɗauka a ƙarƙashin dokar ta ɓacin kan tsaro Nura Ado Suleiman ya tattauna da Kanal Muhd Sani Makiga mai ritaya, masanin tsaro a Tarayyar Najeriyar. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...