Bakonmu A Yau

Janar Sani Kukasheka kan kalubalen tsaron da ke gaban Christopher Musa

Informações:

Sinopse

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da sunan Janar Christopher Musa mai ritaya ga majalisar Dattawa domin amincewar ta ya zama ministan tsaro. Christopher Musa ya yi aiki a matsayin babban hafsan tsaron Najeriya daga ranar 23 ga watan Yunin 2023 zuwa 30 ga watan Octoban 2025, lokacin da shugaban ƙasar Bola Ahmad Tinubu ya yi masa ritaya. Idan majalisa ta amince, Janar Musa zai maye gurbin Badaru Abubakar da ya yi murabus a ranar Litinin. Bayanai sun nuna cewa fannonin da Musa ya fi ƙwarewa a kai shine fatattarkar ƴan ta’adda, da dubarun yaƙi, kasancewar ya yi aiki a matsayin jagoran rundunar sojojin Najeriya da ke kula da tsaron iyakokin Najeriya ta arewa maso gabashi da kuma yankin tafkin Chadi, haka nan ya kuma yi aiki a matsayin guda daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Sierra Leone, da kuma wasu ayyukan a Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya.. Domin sanin tasirin wannan nadin da kuma kalubalen dake gaban Janar Musa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon kakakin run