Bakonmu A Yau

Dakta Nasir Sani Gwarzo akan ranar HIV ta duniya

Informações:

Sinopse

Kamar dai kowace shekara, 1 ga watan Disamba ita ce ranar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta keɓe don yaƙi da cuta mai karya garkuwar jikin ɗan Adam wato HIV ko kuma SIDA.  Bikin na bana ya zo ne a cikin wani yanayi da shugaba Donald Trump ya katse tallafin da Amurka ke bai wa ƙasashe masu tasowa ciki har da na ɓangaren yaƙi da wannan cuta. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Nasir Sani Gwarzo ƙwararren likitan yaƙi da annoba a Najeriya,  wanda ya fara da bayyana halin da ake ciki game da yaƙi da HIV a ƙasar. Ga zantawarsu.