Informações:
Sinopse
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episódios
-
Shu'aibu Mikati akan tasirin barazanar Trump ga tattali arzikin Najeriya
05/11/2025 Duração: 03minBarazanar Shugaban Amurka Donald Trump kan Najeriya na ci gaba da janyo cecekuce a ƙasar da kuma ƙetare, kuma tuni wannan batu ya fara tasiri a musamman kan tattalin arzikin ƙasar. Faduwar hannayen jarin Najeriya da aka gani a wannan mako, ta janyo hankalin mutane yayin da ake ganin kai tsaye yana da alaƙa da barzanar ta Trump. Rukayya Abba Kabara ta tattauna da kwararre kan harkokin tattalin arziki a Najeriya, Alhaji Shu’aibu Mikati kan wannan batu, ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance.
-
Ambasada Abubakar Cika kan barazanar kai wa Najeriya hari da Amurka ta yi
04/11/2025 Duração: 03minYayin da hukumomin Najeriya suka yi watsi da barazanar shugaban Amurka na kai wa ƙasar hari saboda zargin kashe Kiristoci, ƴan kasar da dama na ci gaba da bayyana ra'ayi a kan matsayin na shugaba Donald Trump. Daga cikin waɗanda suka bayyana ra'ayin su a kan wannan barazana har da tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran, Ambasada Abubakar Cika, kamar yadda za ku ji a tattaunawarsu da Bashir Ibrahim Idris.
-
Tattaunawa da Alhaji Shehu Ashaka kan matsalolin tsaro a arewacin Najeriya
03/11/2025 Duração: 03minA Najeriya, babban abin da ya fi ci wa al’ummar yankin Arewacin ƙasar tuwo a ƙwarya ita ce matsalar rashin tsaro, inda hare-haren ƴanbindiga ke ci gaba da haddasa asarar rayukan jama’a, da gurgunta harkar noma da kuma kasuwanci a yankin baki-ɗayansa. Dangane da haka ne Bashir Ibrahim Idris ya zanta da ɗaya daga cikin dattawan yankin Alhaji Shehu Ashaka, ga kuma yadda zantawarsu ta kasance. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
-
Ambasada Muhammad Sani kan rikicin zaɓen Kamaru
31/10/2025 Duração: 03minHar yanzu ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar Kamaru sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka bayyana shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya samu nasara. Shugaban 'yan adawa Issa Tchiroma Bakary da ya zo na biyu ya ƙi amincewa da sakamakon, inda ya buƙaci jama'a da su sake fitowa zanga zanga a ranakun litinin da Talata da kuma Laraba na makon gobe, yayin da a ɓangare ɗaya gwamnati ke barazanar ladabtar da duk wanda ya saɓa dokokin ƙasar, ciki harda shi Isa Tchiroma. Domin tattauna halin da ake ciki a ƙasar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Kamaru a Faransa, Ambasada Muhammadu Sani. Ku alatsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...