Informações:
Sinopse
Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.
Episódios
-
An samu raguwar haihuwa a Najeriya sakamakon rungumar tsarin tazarar Iyali
20/04/2026 Duração: 10minShirin Lafi Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne kan wani rahoton sashen bincike da kula da lafiyar jama’a na NDHS da ke ƙarƙashin hukumar kula da yawan jama’a ta Najeriya NPC, wanda ke nuna cewa daga shekarar 2024 yawan haihuwa ya ragu matuƙa tsakan matan Najeriya daga kashi 5.3 zuwa kashi 4.8. Wannan sakamakon rahoto na NDHS a cewar masana manuniya ce kan yadda mata a yanzu suka rungumi tsarin tazarar iyali bisa dalilai mabanbanta. Kafin yanzu dai, tsarin na tazarar iyali bai samu cikakkiyar karɓuwa a yankin arewacin Najeriya ba, yankin da ke sahun gaba ta fannin yawan haihuwa, sai dai a yanzu alamu na nuna wasu magidantan da kansu ke miƙa iyalansu ga likita don karɓar allura ko magungunan tazarar haihuwar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Yadda Cutar Sankarau ke barazana ga wasu ƙasashen yammacin Afirka
13/04/2026 Duração: 09minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne kan cutar ɗan sanƙarau ko kuma meningitis, cutar da a yanzu haka wasu ƙasashe ke cikin haɗarin fuskantar ɓullarta musamman a yammacin Afrika, waɗanda dama ke a tubalin fuskantar wannan cuta lokaci zuwa lokaci.
-
Kalubalen da ake fuskanta wajan yaki da cutar babban tari ko tuberculosis
06/04/2026 Duração: 10minShirin Lafiya Jarice na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali gameda tarin matsaloli da gangamin yaki da babban tari ke cin karo dasu. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin........
-
Najeriya ta karɓi sabbin alluran rigakafin cutar HIV
30/03/2026 Duração: 10minShirin Lafiya Jari ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan sabbin alluran rigakafin cutar Sida ko kuma HIV Aids da Najeriya ta karɓa ƙarƙashin shirin yaƙi da wannan cuta mai haɗari. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shiri....
-
Haɗarin cizon mahaukacin kare da ke haddasa cutar zangai maras jin magani
23/03/2026 Duração: 09minA wannan makon shirin na lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan matsalar cutar zangai ko cizon mahaukacin kare, cutar dake daɗa bazuwa a jamhuriyyar Nijar musaman a Jihar Maradi, jihar dake sahun gaba wajan masu fama da wannan matsala. Alƙaluman ofishin ministan lafiya na jamhuriyyar Nijar sun nuna cewa cikin mutane 10 da cutar ta kashe, 5 sun fito ne daga jihar Maraɗi, inda aka ga sabbin kamuwa da wannan cuta a tare da mutane har 95. Babban ƙalubalen wannan cuta shi ne rashin maganin iya samun waraka matuƙar aka kamu, ta yadda masu lalurar zasu riƙa haushi da cizo da kuma tirje-tirje irin na kare, yayinda sukan iya yaɗa cutar ga duk wanda suka ciza. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Jita-jitar dake alaƙanta kamuwa da cututtuka ta hanyar amfani da kayayyakin lantarki
16/03/2026 Duração: 09minA wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan jita-jitar da ke alaƙanta amfani da wasu kayakin lantarki a matsayin dalilan da ke sabbaba kamuwa da wasu nau’ikan cutuka ciki har da Cancer.A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan jita-jitar da ke alaƙanta amfani da wasu kayakin lantarki a matsayin dalilan da ke sabbaba kamuwa da wasu nau’ikan cutuka ciki har da Cancer.
-
Cututtukan da ke barazana ga lafiyar jama'a a lokacin azumi
09/03/2026 Duração: 10minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin cututtuka da ke barazana ga lafiyar al'umma a lokacin azumin watan Ramadan, musamman ga masu azumi da ke fuskantar sauye-sauyen lafiyar jiki. Galibi a duk lokacin da aka faro azumi, mutane da dama musamman masu kwantattun cutuka kan taso musamman idan mutane basu ɗauka matakan da suka kamata ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare Azima Bashir Aminu.......
-
Zubar hazo a lokacin zafi ya haddasawa mutane da dama rashin lafiya a Kamaru
02/03/2026 Duração: 10minA wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sauyawar yanayin da wani yanki na arewacin ƙasar Kamaru ya gamu da shi a watan Fabarairun da ya gabata wanda ba safai aka saba ganin faruwarsa ba, ta yadda ake ganin zubar hazo a wani yanayi da kuma ake fama da tsananin zafi, wanda ya haddasa cutuka, lamarin da ya sanya gamayyar masana lafiya dana yanayi jan hankali jama’a don su ɗauki matakan baiwa lafiyarsu kariya. Tsawon kwanaki aka ɗauka hazo na sauka wanda ya mamaye yankuna da dama na arewacin Kamaru dai dai lokaci da zafi ke kaiwa maki 40 zuwa 45 a ma’aunin celsius wanda ya sanya fargabar famtsamuwar cutuka a yanki, lamarin da tuni ya sanya ƙaruwar masu fama da lalure-lalure na lafiya kama daga mura da kuma zazzaɓi har da tashin tsaffin cutukan da ƙura kan tunzura su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Yadda yakamata jama'a su kula da cimakarsu a lokacin azumin Ramadan
23/02/2026 Duração: 10minShirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako zai mayar da hankali kan cimaka a lokacin azumin watan Ramadana, dama yadda wasu ke fuskantar matsaloli masu alaƙa ɓacin ciki sakamakon yanayin ciye-ciyen da akan yi ko dai a lokacin buɗa baki ko kuma sahur. Kamar yadda ya ke bisa al’ada a irin wannan lokaci na azumin watan Ramadan, musulmi kan ƙauracewa abinci da abin sha tun gabanin ketowar alfijir har zuwa bayan faduwar rana, wanda hakan kan jefa masu azumin cikin yanayi na yunwa da kishirwa, sai dai da zarar an buɗi baki mutane kan ci duk abin da suke shawa lamarin da a wasu lokuta kan haddasa ɓacin ciki. A lokuta da dama masana kan gargaɗi jama’a game da cin duk abin da ransu yake so a lokacin da suka buɗi baki, da nufin baiwa lafiyarsu kariya daga cutuka ko lalacewar ciki, dangane da wannan muka nemi ji daga bakin ƙwararru a fannin abinci da amfaninsa a jikin dan-adam. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Najeriya ta ƙaddamar da dokar ta ɓaci a harkar kiwon lafiya
02/02/2026 Duração: 10minA wannan makon shirin zai yi dubi ne kan dokar ta baci a harkan lafiya da gwamnatin Najeriya ta kaddamar inda ta sanar da karuwar cutuka masu alaka da gurbatacciyar iskar da jama’ar ƙasar ke shaka. Hukumar duba gari ta Najeriya ko kuma Environmental Health Council a Turance ita ta sanar da wannan dokar ta baci inda tace munin cutukan dake alaka da numfashi da kuma cutar kansa dake karuwa yasa dole gwamnati da dauki tsauraran matakan, kamar yadda shugaban hukumar Dr Yakubu Muhammad Baba ke cewa. Gurbacewar iska a muhallin ɗan adam kan faru ta hanyoyi da dama kama daga yawaitar hayaƙin da motoci ke fitarwa da kone-konen dazuka ko ƙona itace a gidajen jama’a dama masana’antu da kan fitar da tiriri mai guba, wanda kuma kai tsaye ke cutar da lafiyar ɗan adam tare da haddasa cutuka ko ta’azzarar lalura masu fama da cutukan lumfashi, lamarin da ƙwararren likita Dr Lawal Musa Tahir ke cewa illar gurɓatacciyar iska ta wuce duk inda ake tunani. Ku latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir A
-
An fara gangamin rigakafin cutar Typhoid irinsa na farko a Jamhuriyyar Nijar
19/01/2026 Duração: 09minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan gangamin rigakafin cutar Typhoid da mahukuntan Jamhuriyyar Nijar suka faro a faɗin ƙasar, irinsa na farko da aka taɓa gani a tarihi a wani yanayi da ake ganin ta’azzarar wannan cuta a ƙasar ta yankin Sahel. Wasu alƙaluman hukumar Lafiyar Jamhuriyyar Nijar a 2021 sun ce mutane dubu 30 suka kamu da cutar, a wancan lokaci wadda ta haddasa mutuwar mutane 400. Kodayake a baya-bayan nan babu cikakkun alƙaluman ta’adin cutar, sai dai matakin mahukuntan na fara wannan rigakafi ya nuna tabbacin ta’azzararta. Jihar Agadez na ɗaya daga cikin yankunan da cutar Typhoid ta fi yaɗuwa, kuma tuni aka faro wannan rigakafi da zai shafi mutanen da shekarunsu ya fara daga 1 har zuwa 19 a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.............
-
Illolin da sauyin yanayi ke haifarwa ga lafiyar jama'a
12/01/2026 Duração: 09minA wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali ne kan illolin da sauyawar yanayi ke haifarwa ga lafiyar jama’a, musamman ganin yadda hunturu ya fara amma kuma kwatsam ya ɗauke cikin ƙanƙanin lokaci tare da shigowar zahi, lamarin da ya haddasa cutuka masu yawa a tsakanin jama’a.
-
Ɓullar annobar ƙyanda ta t'azzara a sassan Najeriya
05/01/2026 Duração: 10minA wannan makon shirin tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan fitar wasu sabbin alƙaluman hukumar NCDC masu tayar da hankali matuƙa da ke nuna yawaitar ɓullar cutar ƙyanda ko kuma baƙon dauro dama ƙaruwar mutanen da take kashewa a sassan Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.......
-
Illar ta'ammali da magungunan ƙara kuzari ko rage gajiya da jama'a ke yi
22/12/2025 Duração: 09minShirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan karon ya mayar da hankali kan yadda ɗabi’ar ta’ammali da wasu nau’ikan tsumin gargajiya da sunan samun kuzari ko kuma ƙarfin jiki ke ci gaba da ta'azzara tsakanin jama'a, wanda masana suka yi ittifaƙin na da matuƙar illa ga lafiyar jama’a. Tsumi na baya-bayan nan da ke samun karɓuwa tsakanin jama’a musamman masu ayyukan ƙarfi shi ne ‘’Wankin ciki’’ ko kuma Gyaran Gida ko kuma Aji Garau kamar yadda wasu ke kiranshi, tsumin da ke ɗauke da magungunan gargajiya, kuma ya ke ci gaba da samun karɓuwa tsakanin dukkanin rukunin mutane kama daga matasa da kuma magidanta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Dabarun yaƙi da ƙibar da ta wuce ƙima ko kuma Obesity tsakanin matasa
15/12/2025 Duração: 09minShirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir a wannan mako ya mayar da hankali kan wasu alƙaluman mujallar Lancet da ke nuna cewa nan da shekarar 2050 fiye da kashi 50 na yawan al’ummar Afrika musamman Afrika za su zama masu ƙibar da ta wuce ƙima ko kuma Obesity a turance. Alƙaluman na Lancet wanda aka tattara bayan gwaji a ƙasashe fiye da 50 ya nuna cewa matsloli masu alaƙa da cimaka da kuma rashin motsa jiki su ke matsayin kan gaba da za su haddasa wannan matsala ta Obesity ko kuma ƙibar da ta wuce ƙima. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Bincike ya gano cewa kashi 38 na matan Damagaram ne kaɗai ke haihuwa a asibiti
08/12/2025 Duração: 10minShirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali game da yadda wasu mata a Jamhuriyyar Nijar ke ƙin amincewa da haihuwa a asibiti duk kuwa da haɗarin da ke tattare da haihuwa a gida. Wasu alƙaluman baya-bayan nan da mahukuntan jihar Damagaram suka tattara, ya nuna cewa ƙasa da kashi 40 na mata ne ke haihuwa a asibiti duk kuwa da yadda mahukunta suka mayar da haihuwar kyauta a asibitocin jihar waɗanda aka samar da su a gab da jama'a. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Kamaru ta yi nasarar rage mutuwar mata yayin haihuwa a cikin shekaru 4
01/12/2025 Duração: 10minA wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan wasu alƙaluma da ke nuna cewa cikin shekaru 4 da suka gabata Kamaru ta yi nasarar rage yawan matan da ke mutuwa a lokacin haihuwa ko kuma goyon ciki. Alƙaluman hukumar kula da lafiyar yara da na DHS mai tattara alƙaluman jama’a sun nuna da cewa da kusan rabi ne aka samu raguwar mace-macen matan, inda daga mace-macen mata dubu 2 cikin dubu 100 a 2018 adadin a yanzu ya dawo mace-macen mata 406 cikin dubu 100 duk shekara wanda ke nufin gagarumar nasara, kodayake ministan lafiya na ƙasar Manaouda Malachie ya ce sun yi amfani da wasu tsare-tsare gabanin samun wannan nasara.
-
Fahimtar ƙwararru game da tasirin Hamma ga lafiyar ɗan adam
24/11/2025 Duração: 09minShirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir a wannan makon ya mayar da hankali kan wasu daga cikin ɗabi’un jikin ɗan adam da kan faru ba tare da shiri ba, cikin waɗannan ɗabi’u kuwa har da hamma, inda shirin zai duba tasirinta ga lafiyar ɗan adam. Rubuce-rubucen masana game da ɗabi’ar ta hamma na alaƙanta ta da barci ko gajiya ko kuma yunwa, sai dai fa masanan sun kuma bayyana cewa Hammar na taka muhimmiyar rawa a tsarin lumfashin ɗan adam, musamman ta fuskar daidaita yawan iskar da mutum ke shaƙa wato Oxygen da kuma wadda ya ke fitarwa wato Carbon dioxide. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Yadda cutar Suga ke mamaya a ƙasashen Afrika
17/11/2025 Duração: 10minShirin lafiya jari ce na wannan mao ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da ke cewa mutane akalla miliyan 24 ne ke fama da cutar Suga a Nahiyar Afrika kawai. Wannan kuwa na faruwa ne a dai-dai lokacin da cutar ke sauya salo da tsanani ga masu fama da ita, baya ga bijirewa magani. Danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
-
Mutane fiye da dubu 28 na mutuwa duk shekara saboda gurɓacewar iska a Ghana
10/11/2025 Duração: 10minA wannan makon shirin Lafiya jari ce ya mayar da hankali kan wani bincike a Ghana da ke nuna yadda mutane sama da dubu 28 ke mutuwa duk shekara saboda gurbacewar iska. Alƙaluman hukumar kula da Lafiya ta Ghana ne ke sanar da wannan adadi, wanda kai tsaye ke nufin duk mintuna 19 wannan matsala ta gurɓatacciyar iska kan sabbaba mutuwar mutum guda a wannan ƙasa ta yammacin Afrika, batun da ke buƙatar kulawar gaggawa don ɗaukar matakan da suka dace. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...