Lafiya Jari Ce

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editora: Podcast
  • Duração: 4:01:19
  • Mais informações

Informações:

Sinopse

Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.

Episódios

  • Akwai alaƙar mai ƙarfi tsakanin cutar yunwa da taɓuwar ƙwaƙwalwa

    27/10/2025 Duração: 10min

    Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya mayar da hankali kan alaƙar cutar yunwa da kuma lafiyar ƙwaƙwalwa, inda a cikin shirin zakuji yadda masana a ɓangaren suka alakantawa waɗannan matsaloli biyu a matsayin lalurori masu tafiya kafaɗa da kafaɗa da juna. A kowacce ranar 10 ga watan Oktoba ne duniya ke gudanar da gangamin kula lafiyar ƙwaƙwalwa don bikin ranar ta lafiya ƙwaƙalwa ko kuma World Mental Health Day a turance, da nufin wayar da kai game da muhimmancin lafiyar ƙwaƙwalwa dama matsalolin da ka iya barazana ga ƙwaƙalwa, sai dai a wannan karon ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa ta MSF ta alaƙanta ƙarancin abincin mai gina jiki da ke haddasa cutar da yunwa da matsalar ƙwaƙwalwa...... wannan shi ne maudu’in da shirin Lafiya Jari ce na wannan mako zai mayar da hankali akai, sai ku biyo mu.... Wani rahoto da MSF ta fitar a ranar ta 10 ga wata ta koka da ƙaruwar yaran da ke fama da cutar yunwa sakamakon ƙarancin abinci mai gina jiki, wanda ta ce matsala ce kai tsaye da ke shafar lafiya

  • An gudanar da gangamin wayar da kai akan cutar daji a Jamhuriyar Nijar

    20/10/2025 Duração: 10min

    Kowanne watan Oktoba, lokaci ne da ɓangarorin lafiya a Jamhuriyyar Nijar ke amfani da shi wajen gudanar da gangamin wayar da kai a ƙasa baki ɗaya game da cutar sankara ko kuma Cancer wadda ake ganin ƙaruwar masu kamuwa da ita a sassan wannan ƙasa ta yankin Sahel,,,, wannan shi ne maudu’in da shirin na Lafiya jari ce zai mayar da hankali akai sai ku biyomu. Jamhuriyyar Nijar na ganin sabbin kamuwa da cutar ta cancer dubu 9 da 787 duk shekara ciki kuwa har da mata masu kamuwa sankarar mama dubu 2, wanda ke matsayin wani ɓangare na jumullar mata miliyan 2 da dubu 300 da ke kamuwa da sanakarar maman duk shekara a sassan duniya bisa alƙaluman hukumar WHO.

  • Yadda Cholera ta kashe mutane kusan dubu 5 a sassan Najeriya cikin shekaru 5

    13/10/2025 Duração: 10min

    Shirin a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan yawaitar samun cutar Kwalara ko kuma amai da gudawa  a sassan Najeriya, cutar da a baya-bayan nan ta kashe ɗimbin al'umma a ƙasar mafi yawan jama'a a Nahiyar Afrika. Wasu alƙaluma da hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasar NCDC ta fitar sun nuna cewa mutane kimanin dubu biyar (5,000) cutar ta kwalara ta halaka a sassan Najeriyar daga shekarar 2020 zuwa 2025 da muke ciki. Latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir Aminu.............

  • Cutar Hanta ta Hepatitis nau'in B na yaɗuwa kamar wutar daji a Najeriya

    06/10/2025 Duração: 10min

    Shirin a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan ciwon hanta nau’in B ko kuma Hepatitis B a turanci, cutar da masana ke gargaɗi game da yadda ta ke yaɗuwa kamar wutar daji tsakanin jama’a. Wasu alƙaluma sun nuna yadda ake da mutum fiye da miliyan 257 da ke fama da wannan cutar, a wani yanayi da Najeriya ke sahun ƙasashe 5 masu ɗauke da kashi 60 na masu wannan cuta a duniya baki ɗaya. Masana a ɓangaren lafiyar Najeriya sun bayyana yadda wannan cuta ta Hepatitis B ke yaɗuwa kamar wutar daji a sassan ƙasar, kuma abin dubawar shi ne yadda mutane da yawa ke rayuwa da cutar yanzu haka ba tare da sanin suna ɗauke da ita ba, kan hakan kuma muka nemi ji daga masana irin Dr Misbahu Sahabi na Cibiyar Kiwon Lafiya ta tarayya da ke garin Birnin Kudun jihar Jigawa, wanda ke cewa tun farko cutar na da rabe-rabe wato mai haɗari da kuma mai sassaucin illa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

página 2 de 2