Informações:
Sinopse
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.
Episódios
-
Ƴan Najeriya na ci gabata da cece-kuce kan sabon bashin da gwamnati ta ciyo
04/06/2025 Duração: 10minShirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan wani sabon bashin da Najeriya ta ciwo daga bankin duniya da ya haura sama da dala biliyan ɗaya. Wannan sabon bashin dai ya janyo cece-kuce daga ƴan ƙasar waɗanda suka nuna damuwa kan yadda gwamnati ke ci gaba da ciyo manyan basussuka duk da iƙirarinta na janye tallafin manfetur domin dogaro da kai. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba............
-
Yadda matan Arewacin Najeriya ke ƙara yin tasiri a kasuwancin jihar Lagos
28/05/2025 Duração: 13minShirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne kan babban taron da ƙungiyar Matan Arewa ƴan kasuwa mazauna Lagos da ke kudancin Najeriya su ka yi a birnin Lagos, wanda ya mayar da hankali kan karfafawa mata gwiwa kan harkokin kasuwanci da bunkasa tattalin arzikinsu.
-
Yadda karancin wutan lantarki ke kokarin durkusar da masu masana'antu a Najeriya
14/05/2025 Duração: 10minShirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan makon tare da Ahmed Abba ya yi duba kan irin girman asarar da masau kamfanoni su kace sun tafka saka makon matsalar karancin wutan lantarki da ake fama da ita musamman a arewacin kasar. Ku shiga alamar sauti domin jin cikakken shirin......