Informações:
Sinopse
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.
Episódios
-
Borno na son farfado da tattalin arzikin waɗanda ricikin Boko Haram ya ɗaiɗaita
14/10/2026 Duração: 10minShirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin jihar Borno da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al'ummar da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita. Bayan kwashe shekaru da dama na rikicin Boko Haram da kuma tasirinsa ga tattalin arziki, gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na neman wata hanya ta bunƙasa tattalin arzikinta da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al'ummarta. Wannan ne ya sa gwamnatin jihar ta haɗu da masu zuba jari da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki a wani taro da aka gudanar a Legas, domin duba damar zuba jari da za ta taimaka wajen samar da abin da ake kira durable solutions, wato hanyoyin magance matsalolin al'umma na dogon lokaci. A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta sanar da cimma alkawuran zuba jari har guda tara bayan kammala taron tattaunawa da aka gudanar a Legas Kamfanin Dangote ya ware hannun jari na darajar
-
Rahoton CBN ya ce ƙarfin sayayyar ƴan Najeriya ya ƙaru a watan Satumba
07/10/2026 Duração: 10minYau shirin zai mayar da hankali kan sabon rahoton Babban Bankin Nigeria, wanda ya fito da sabbin alkaluman ci gaban da aka samu a fannin damar iya sayen kayayyaki a kasuwanni a tsakanin al’ummar kasar da ya karu da maki 53 a watan Satumba daga maki 52.7 daga watan Agustan da ya gabata. Madallah! Lallai za’a yi cewa, tattalin arzikin Najeriya na farfadowa bisa alƙaluma, amma ga talakan ƙasar, har yanzu babu wani alamun sauƙi. A kasuwanni, farashin kayan abinci da sauran kayayyaki na ci gaba da kasancewa babban ƙalubale, yayin da ’yan kasuwa ke kokawa da tsadar sufuri da wutar lantarki..
-
Dalilin da ya sanya aka fara haramta sana'ar jari bola a wasu sassan Najeriya
30/09/2026 Duração: 10minSana’ar tattara wa da sayar da tsofaffin ƙarafa da sauran tarkace wadda aka fi sani da ‘Bola Jari’ na daga cikin sana’o’i da dubban mutane masamman matasa ke dogaro da su a Najeriya. Amma a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sana’ar ta fuskanci babban ƙalubale, musamman saboda zargin cewa wasu masu tattara ƙarafa na amfani da ita wajen sayar da kayayyakin da aka sace daga tituna, gadoji, layin dogo da sauran muhimman abubuwan more rayuwa. Wannan ne ya sa wasu gwamnatocin jihohi suka ɗauki matakin dakatarwa ko haramta sana’ar baki ɗaya. Yanzu haka Ƙungiyar masu sana’ar ta jari bola ta yi barazanar tsunduma yajin aikin gargaɗi, ta hanyar dakatar da lodi ko sayar wa kamfanoni baraguzai da suke tattarawa. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Matatar matatar Ɗangote ta ƙaddamar da sayar da hannayen jarinta a hukumance
16/09/2026 Duração: 10minShirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan ƙaddamar da shiga matatar Ɗangote kasuwannin hannayen jarin Najeriya, a wani biki da aka gudanar a babban shelkwatan kasuwannin hannayen jarin Najeriya da ke Marina a birnin Legas, inda shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko da kansa ya kaɗa ƙararrawar buɗe shigar matatar a hukumance. Matatar ta sanya hannun jari biliyan 4 da miliyan 100 kasuwa, kan Naira 525 ga kowane guda, inda take fatan tara kusan Naira tiriliyan 2 da biliyan 150. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..............
-
Tasirin da saida hannun jarin matatar man Dangote ke da shi ga al'umma
09/09/2026 Duração: 09minShirin kasuwa akai miki dole na wannan lokacin, ya maida hankali ne kan yadda matatar Dangote ta shirya buɗe ƙofifinta ga al’umma domin su mallaki wani kaso a matatar mafi girma a Afirka, bayan da a karon farko ta sanar da shiga kasuwar hannayen jari. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........
-
Sharhi kan kalaman Alhaji Atiku na maido da tallafin mai a Najeriya
02/09/2026 Duração: 10minShirin ‘kasuwa akai miki dole’ a wannan mako tattauna ne kan wasu batutuwa da suka taso masu nasaba da siyasa da tattalin arziƙi a Najeriya, Inda muhawara ta kaure kan batun tallafin man fetur, bayan da ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar adawa ta ADC Alhaji Atiku Abubakar ya yi alƙawarini maido da tallafin man idan aka zaɓe shi a 2027, to amma nan da nan gwamnatin Najeriyar ta mayar da martani. Kalaman Atiku, sun tayar da kura tare da ƙara zafafa lamura a fannin siyasa da tattalin arzikin ƙasar, inda a ƙarshe, shugaba Bola Ahmed Tinubu, da kansa, ya fito ya soki lamarin. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmad Abba...............
-
Ghana ta zama ƙasa ta 6 a cikin jerin ƙasashen da ke samar da zinari a duniya
26/08/2026 Duração: 10minShirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda Ghana ta zama ta shida a cikin manyan ƙasashe da suka fi samar da zinare a duniya, bayan zarce Amurka a alƙaluman yawan zinare da ƙasar ta yammacin Afirka ta hako a shekarar 2025 da ta gaba. To, amma menene tasirin kasancewar ƙasar ta ɗaya daga cikin manyan masu samar da zinare a duniya ke nufi ga talakawan Ghana da kuma tattalin arzikin ƙasar? Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmad Abba............
-
Me cigaban kasuwar hannayen jarin Najeriya ke nufi ga talakan ƙasar kashi na 2
19/08/2026 Duração: 09minShirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya dora kan shirin makon da ya gabata, wanda ya mayar da hankali kan ci gaba da kasuwar hannayen jarin Najeriya ta samu, wajen zama ta ɗaya a duniya, kamar yadda mujallar Bloomberg ta sanar a ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026. To amma me cikin gaban kasuwar hannayen jarin ke nufi ga takan ƙasar?
-
Cigaban kasuwar hannayen jari na nufin rayuwa ta fara inganta ga talakan Najeriya?
12/08/2026 Duração: 09minA ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026, mujalar Bloomberg da ke bibiyar harkokin tattalin arzikin ƙasashen duniya, ta bayyana kasuwar hannayen jarin Najeriya a matsayin ta ɗaya a duniya a fannin dala, wajen yi wa ta Koriya ta Kudu fintinƙau. Masana tattalin arziki sun alakanta wannan gagarumin ci gaba da kasuwar ta samu da sauye-sauye masu tsauri da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi a fannin tattalin arziki.
-
Ghana ta yiwa ƙasashen Afrika fintinkau a fannin ci gaban hada-hadar kuɗaɗe ta wayar hannu
05/08/2026 Duração: 10minShirin na wannan mako ya duba yadda Ƙasar Ghana ta zama jagaba a fannin hada_hadar kuɗi ta wayar hannu a Afirka, inda a wannan shekara kaɗai kamfanonin sadarwar wayar tafi da gidanka suka yi hada-hadar sama da Cidi biliyan 40. Ku danna lamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
-
Illar cushen kusan naira tiriliyan 1 a kasafin kuɗin Najeriya ga tattalin arziƙi
29/07/2026 Duração: 09minShirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, ya mayar da hankali ne kan yadda aka gano cushen kusan Naira triliyan ɗaya cikin kasafin kuɗin Najeriya na wannan shekarar ta 2026, domin sayen motocin alfarma da kuma ayyukan tallafa wa jama'a. Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton da wata cibiyar da ke sa’ido kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen kasafi a Najeriya wato Tracka. Cibiyar ta ce adaɗin ya zarce jimillar kuɗin da aka ware wa manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya guda bakwai. Batu da ya janyo ce-ce-ku-ce. A cikin rahotonta, Cibiyar ta nuna cewa gwamnatin ta ware kusan Naira biliyan 960 ga ma'aikatun Sufurin Jiragen Sama, Gidaje, Harkokin Mata, Ciniki da Masana'antu, Shari'a, Kiwon Dabbobi da Albarkatun Man Fetur, amma kuma ta ware kusan Naira biliyan 963 domin sayen motoci da kuma ayyukan tallafa wa jama'a. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
-
Matakin matatar Ɗangote ya fusata ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya
22/07/2026 Duração: 10minShirin a wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi dubi ne kan matakin da ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta sanar na dakatar da sayen mai daga matatar Dangote, sakamakon matakin da matatar ta ɗauka na fara sayar musu da man da take tacewa da dala maimakon Naira. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
-
Rashin rassan bankuna ya tilastawa al'ummar karkara rungumar POS a Najeriya
08/07/2026 Duração: 09minShirin kasuwa akai miki dole dake bibiyar harkokin kasuwanci da tattalin arziki na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ci gabar fasahar zamani da aka samu a fannonin haɗar-haɗur ƙudi a Najeriya, ke shafar al’ummomi a yankunan ƙarƙara.
-
Ana samun ƙaruwar cin bashin kuɗin kiran waya tsakanin jama'ar Najeriya
01/07/2026 Duração: 10minShirin "Kasuwa Akai Miki Dole" na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya suka rungumi ɗaukar bashin kiran waya, wanda wani rahoto ya ce, a bara kaɗai anci bashin kiran waya da ƙudinsu ya kai Naira Tiriliyan 4 da biliyan 61. Wasu bayanai da cibiyar fintech firms Optasia mai tattara alƙaluman shige da ficen kuɗaɗen layukan sadarwa ta fitar a baya-bayan nan, ya nuna yadda ƴan Najeriya waɗanda ke amfani da wayar hannu, a kullum ke tururuwar ciwo bashin katin kira wanda ke ɗauke da kuɗin ruwa. Rahoton cibiyar ya ce a shekarar 2025 kawai ƴan Najeriya sun ci bashin katin kiran waya da ya kai Dala biliyan 3 da miliyan 18 kwatankwacin Naira tiriliyan 4 da biliyan 61, abinda ke haskawa ƙarara cewa adadin ya ƙaru da kaso 12.3 cikin 100 idan an kwatanta da shekarar 2024, wadda ya kasance Naira tiriliyan 4 da biliyan 38. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Yadda tattalin arzikin Ghana ke haɓɓaka sannu a hankali
17/06/2026 Duração: 09minYau shirin ya mayar da hankali ne dangane yadda tattalin arzikin ƙasar Ghana ke ci gaba da ɓunƙasa sannu a hankali. Ku danna alamar sauraro domin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
-
Koken ƴan Najeriya kan yadda bankuna ke zare musu kuɗi daga asusun ajiyarsu
20/05/2026 Duração: 10minShirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan yadda ƴan Najeriya, ke nuna fushinsu dangane da zargin cire musu kuɗi ba bisa ka’ida ba daga asusun bankunansu. Miliyoyin 'yan Najeriya da yanzu haka ke fuskantar hauhawan farashin kayayyaki da kuɗin sufuri, da kuma rashin tabbas ga makomarsu a fannin tattalin arziki, caje-caje da dama da bankuna ke yi a asusun ajiyarsu na sake jifasu cikin damuwa. A cikin 'yan watannin nan, koke-koke sun mamaye kafofin sada zumunta, sakamakon rashin karin bayani kan yawaitan kudaden da bankunan ke cirewa.. Duk da cewa bankuna sun dage cewa hakan tsari ne da kuma sahalewar haka daga babban bankin kasar CBN, kwastomi na diga ayar tambaya kan cirewa fiye sau ɗaya kan, ko kuma daga wanda ya tura da kuma wanda ya ƙarba, yayin da wasu ke kokawa kan rashin maida musu kudinsu nan take idan aka samu masalar sabis kudi bai je ga wanda aka tura ba da dai sauransu... Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Yadda ƴan kasuwa a Najeriya suka jingine harakokinsu saboda tsadar sufuri
13/05/2026 Duração: 10minShirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
-
Yadda tsadar sufuri ya tilastawa 'yan kasuwa jingine sana'o'insu a Najeriya
13/05/2026 Duração: 10minA yau shirin ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Sannu a hankali, irin hada-hadar da aka saba gani tsakanin mafi yawan kasuwannin Nigeria na neman zama abun tarihi, sakamakon yadda ‘yan kasuwa masu tarin yawa suka jingine harkokinsu na kasuwanci saboda tsadar sufuri. ‘Yan kasuwa, na kukan samun wagegen gibi tsakanin uwar kudin jarinsu da abinda suke kashewa na safarar kayansu zuwa kasuwanni, saboda tsadar kudin sufuri da kuma rashin ciniki saboda halin rashin kudi da ‘yan kasar ke ciki. Kasancewar kowane sasshen Nigeria na da nau’in kayayyakin da yake da su a wadace, ‘yan kasuwa daga arewacin kasar, kan saro kayayyaki irin su Manja da Man Gyada da Garin Kwaki da makamantan su, daga kudancin kasar, yayinda ‘yan kasuwa daga kudanci, kan sayi hatsi, dabbobi da makamantan su daga arewacin kasar. Bayanan hukumar kididdiga ta Nigeria, sun yi nuni da cewa damar ikon sayen kay
-
Damarmaki da kuma ƙalubalen da manoman Albasa a arewacin Kamaru ke fuskanta
29/04/2026 Duração: 09minShirin kasuwa akai miki dole na wannan makon, ya duba ƙalubale da kuma damammaki a ɓangaren noman albasa a arewacin Kamaru. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
-
Matakan da bankin CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗi a Najeriya
22/04/2026 Duração: 10minShirin Kasuwa akai miki doke na wannan mako ya yi duba ne kan matakan da babban bankin Najeriya CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗaɗe, domin rage hauhawan farashin kayayyaki a kasuwanni da kuma daga darajar kuɗin ƙasar wato Naira, ta hanyar rage kuɗaɗe da ke yawo a hannun jama’a. Babban Bankin Nigeria, ya fito da bakin alƙalamin adadin kuɗaɗen da ke bankuna da waɗanda ake hada-hada da su a cikin ƙasa tare da waɗanda jama’a ke jujjuyawa a hannunsu. Adadin wannan kudi dai a cewar bankin na CBN, ya kai Naira Triliyan 123 da biliyan 15, a watan Fabareiru, inda aka samu raguwar adadin madarar kuɗi da ke hannun jama’a akan na watan Janairu, wanda ya kai Nera Triliyan 123 da biliyan 36. Haka ma adadin kudaden kasar a asusun ajiyarta na ketare ya ragu zuwa Nera Triliyan 28 da biliyan 41 daga Nera biliyan 29 da biliyan 61. Ku latsa alamar sauti don sauti don sauraron cikkan shirin tare da Ahmad Abba.............