Ilimi Hasken Rayuwa

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editora: Podcast
  • Duração: 3:57:54
  • Mais informações

Informações:

Sinopse

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.

Episódios

  • Yadda Nijar ta bijiro da sabon tsarin karatu na bada ƙarin horo lokacin hutu

    09/09/2025 Duração: 09min

    Shirin ilimi Hasken rayuwa na wannan rana ya mayar da hankali ne kan tsarin koyarwa da Nijar ke yi na baiwa dalibai karin horaswa akan darussa masu wahala a lokutan hutu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

  • Matakin gwamnatin Najeriya na dakatar da kafa makarnatun gaba da sakandare

    02/09/2025 Duração: 10min

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako ya duba matakin gwamnatin Najeriya na dakatar da kafa makarantun gaba da sakandare a fadin ƙasar har na tsawon shekaru 7, mataakin da ya biyo bayan wani zama da majalisar zartaswar ƙasar ta yi a ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu. Majalisar ta ce babu amfanin kafa makarantun da ba za a samu abin da ake buƙata ba, a maimakon haka zai kyautu a inganta waɗanda ake da su.

  • Makarantun Firamare sun fara koyarwa da harshen Hausa don sauƙaƙa koyo a Kano

    26/08/2025 Duração: 09min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda wasu daga cikin Makarantun Firamare a jihar Kano suka koma koyarwa da harshen Hausa da nufin sauƙaƙa koyo da koyarwa tsakanin yaran jihar. Kafin yanzu dai akwai dokar da ta soke koyarwa da harsunan gida 3 a Makarantun Najeriyar da suka ƙunshi Hausa da Yarabanci da kuma Igbo, inda tuni aka ga yadda wasu Makarantu suka daina koyarwa da wannan harshe, kodayake tun tuni dama yankin kudancin Najeriya ya yi watsi da wannan doka tare da ci gaba da koyar da harsukan. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

  • Tsarin cigaban manyan malaman jami'a a Jamhuriyar Nijar

    19/08/2025 Duração: 09min

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai duba tsarin cigaban manyan malaman jami'a a Jamhuriyar Nijar, wanda ke kai su ƙololuwa a harkar ilimi. Domin samun ingataccen ilimi, dole ne a samu ƙwararrun malamai da za su koyar da ɗalibai da ke karatu a fannoni dabam-dabam. haka zalika malaman da ke koyarwar su ma su na neman hanyoyin ƙara ƙwarewa don kai wa ƙololuwa a aikin na su na koyarwa.

página 2 de 2