Informações:
Sinopse
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Episódios
-
Yadda Real Madrid ta doke Barcelona da ƙwallo 2 da 1 a haɗuwar El Classico
27/10/2025 Duração: 10minShirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya nazarci yadda aka yi fafatawa mai cike da armashi tsakanin Barcelona da Real Madrid wato haɗuwar hamayya tsakanin manyan ƙungiyoyin na Spain guda 2 karawar da ake kira El-Classico. Yayin haɗuwar ta wannan karo dai, Real Madrid ce ta yi nasara da ƙwallaye 2 da 1 duk da ya ke wasan ya gudana ne a gidanta wato filinta na Santiago. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
An fara gasar Super Ligue ta Jamhuriyar Nijar
20/10/2025 Duração: 09minShirin duniyar wasanni na wannan mako zai maida hankali a kan yanda aka fara gasar ligue ta ƙasar Niger da ake ma lakabi da SUPER LIGUE. A ƙarshen mako ne aka faro gasar Lik ta Jamhuriyar Nijar wacce ake wa laƙabi da Super Ligue.Ita dai wannan gasa ta Super League ta kasance kololuwar gasar kwallon ƙafa a ƙasar, inda ta ke ƙumshe da ƙungiyoyi 16, kuma babban birnin ƙasar Niamey ka dai na da club 12. A tsarin wasan kowa zai kara da kowa a gida da waje kamar yanda ake yi a sauran ƙasashe ke nan kowace ƙungiya za ta yi wasa 30. Haka kuma kamar a sauran ƙasashe zakaran da ta lashe wannan gasar za ta wakilci ƙasar a gasar ligue a matakin nahiyar Afrika da hukumar Caf ke shirya, don haka ɗaukacin waɗannan club ɗin ke maida hankali don ganin sun taka rawar gani a gasar. Kafin mu tsunduma cikin shirin bari muyi ratse don yin ɗaurayar yadda gasar ta gudana a bara tare da Magaji Minista mai sharhi ne kan harakar wasannin kwallon kafa.
-
Makomar ƙasashen Najeriya, Senegal da Afrika ta Kudu a gasar cin kofin Duniya
13/10/2025 Duração: 09minShirin a wannan mako ya mayar da hankali ne kan wasannin neman tikitin zuwa gasar cin kofin Duniya ta 2026 da ƙasashen Amurka, Mexico da Canada za su karɓi baƙunci. A Nahiyar Afrika tuni dai wasu ƙasashe suka sami tikitin zuwa gasar da suka haɗar da Morocco da Tunisia da Aljeriya da Ivory Cost, sai dai ƙasashen Najeriya da Afrika ta Kudu da kuma Senegal na cikin halin rashin tabbas, sai dai a wannan Talata ne za su san makomarsu. Latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abubakar Isah Ɗandago..................
-
Gudummawar da cibiyoyin horar da matasa ke baiwa ƙwallon Ƙafa a Najeriya
06/10/2025 Duração: 09minShirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan lokaci za yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon Ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Najeriya. A wani bangare na gudummawarsu ga ci gaban wasan kwallon kafa a Nigeria, ɗai-ɗaikun jama’a da ƴan kasuwa kai harma da tsofin ƴan wasan tawagar Super Eagles ta ƙasar, sun fara kafa cibiyoyi masu zaman kan su, da su ke zakulowa tare da horar da matasa don yin fice a harkar ta kwallon ƙafa. Irin wadannan cibiyoyin horar da matasa wasan na kwallon kafa da a turance ake kira FOOTBALL ACADEMY, kan shiga birane da karkara don tuntubar ƙanana da matsakaitan club-club, domin samun ƴan wasan daga wajen su da za a yi rijistarsu a wannan cibiya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..