Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editora: Podcast
  • Duração: 3:48:58
  • Mais informações

Informações:

Sinopse

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episódios

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabambanta

    17/04/2026 Duração: 10min

    Yau  juma'a, rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tattalin arziƙin, siyasa, zamantakewa da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabambanta...

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan biyan bashin Triliyan 3 da Najeriya ta yiwa fannin lantarki

    07/04/2026 Duração: 10min

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da ware sama da Naira tiriliyan uku domin biyan bashin da ke wuyan ƙasar a ɓangaren wutar lantarki. Sanarwa daga fadar shugaba Bola Tinubu ta ce an ɗauki matakin ne bayan an yi bitar illahirin bashin da ke wuyan gwamnati tsakanin 2015-2025 wannan bashi biyan wannan bashi zai bayar da damar shawo kan mafi yawan matsalolin da ke haifar da ƙarancin wutar lantarki a Najeriya. Shin ko meye ra’ayoyinku a game da wannan mataki? Ko wataƙila hakan zai kai ga ƙara ingantar samar da wutar lantarki a Najeriya? Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare na Nasiru Sani

  • Ra'ayoyin masu saurare kan dokar samar da mataimakin shugaban ƙasa a Kamaru

    06/04/2026 Duração: 10min

    Majalisun dokokin Kamaru sun amince da dokar da ke bai wa shugaba Paul Biya damar ƙirƙiro muƙamin mataimakin shugaban ƙasa da ke iya maye gurbin shugaban idan buƙatar hakan ta taso. Wasu dai na kallon hakan a matsayin yunƙurin da Biya ke yi domin tsara wanda zai gaje shi, a daidai lokacin da ake gaba da ɗiga ayar tambaya dangane da yanayi lafiyar shugaban mai shekaru 93 a duniya. Ku danna alamar sauraro dimin jin cikakke shirin tare da Nasiru Sani.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan yadda yaƙin Gabas ta tsakiya ya haddasa tsadar kayan masarufi

    23/03/2026 Duração: 10min

    An shiga mako na huɗu da barkewar rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya, inda ɓangarorin da ke hannu a rikicin ke ci gaba da kai wa juna hare-hare tare da kashe mutane da kuma lalata cibiyoyin makamashi. Tuni dai hakan ya haifar da tashin goron zabi ga farshin abubuwa da dama sanadiyar hauhawar farashin mai a kasuwar duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Yusuf

  • Ra'ayoyin masu saurare kan matakin CAF na kwace nasarar AFCON daga Senegal

    19/03/2026 Duração: 10min

    Hukumar kwallon ƙafar Afrika ta sanar da ƙwace Kambun da Senegal ta lashe a gasar neman kofin nahiyar da aka kammala cikin watan Janairun da gabata tare da miƙa shi ga ƙasar Moroko. Wannan dai mataki ne da ya yi matuƙar girgizar masu shawar harkar ƙwallon ƙafa a sassan duniya, inda tuni Senegal a buƙaci a gudanar da bincike bisa zargin cewa akwai yiyuwar an bayar da rashawa ne don ƙwace wannan galaba. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Yusuf.

  • Yadda farashin makamashi ya yi tashin gwauro zabi a duniya

    12/03/2026 Duração: 09min

    Yanzu haka farashin ɗanyen man fetur na ci gaba da hauhawa sakamakon yaƙin da Amurka da Isra’il suka ƙaddamar kan Iran, inda yanzu haka ake sayar da gangar mai fiye da dala 92 a kasuwar duniya. A wannan yanayi dai ko shakka babu, ƙasashe masu arzikin mai ne irinsu na Najeriya za su ci moriyar wannan rikici. Shiga alamar sauti, domin suararon cikakken shirin.

  • Yadda yaƙin Gabas ta Tsakiya ya haifar da tsadar makamashi a duniya

    04/03/2026 Duração: 09min

    A yayin da yaƙi tsakanin Isra’ila da Amurka da Iran ke daɗa rincaɓewa, an fara gani tasirinsa a kasuwar ɗanyen mai da makamashi ta duniya. Ko a Najeriya, ƙasar da ta fi arziƙin ɗanyen mai a Afirka, farashin litar fetur ya tashi, kuma masana sun ce ana iya ganin cigaba da tashin farashin makamashi. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan harajin yin wa'azi da ƴan bindiga suka sanya a Kebbi

    23/02/2026 Duração: 10min

    A Najeriya wata ƙungiyar ta'addanci da ba’a kai ga tantace wa ba, ta buƙaci a’ummar Utono ta ƙaramar hukumar Ngaski a jihar Kebbi da ta biya su zunzurutun ƙudi har Naira miliyan 100, kafin su bai wa malamai damar gudanar da Tafsiri ko wa’azi a wannan watan Azumi na Ramadana. Ƴan ta'addar sun bayyana bukatar ne a wata rubutacciyar wasika da suka aika garin na Utono. Wannan dai shine karon farko da wata ƙungiya da bukaci malamai biyan wani kudi domin gabatar da wa’azi, ko da ya ke al’umma a wasu yankunan sun saba biyan kudi don neman yancin walwa, ko ayyukan noma ko ma girɓi. Yaya kuke kallon wannan sabon bukata na ƴan ta‘adda? Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan fargabar fuskantar ƙarancin abinci saboda gobarar Singa

    19/02/2026 Duração: 10min

    Dai dai lokacin da al’ummar musulmi suka faro azumin watan ramadana, can a jihar kano ta arewacin Najeriya da sauran jihohi maƙwabtanta, jama’a ne suka shiga cikin fargabar yiwuwar fuskantar hauhawar farashin kayakin masarufi sakamakon mummunar ɓarnar da gobara ta yi a kasuwar singa da ya haddasa ƙarancin kayakin na masarufi a kasuwannin jihar, kasancewar kasuwar ta singa babbar kasuwar da ke samar da kayakin Masarufi a kusan dukkanin arewacin Najeriyar dama wasu ƙasashen maƙwabta. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Muhammad Ɗan Bauchi.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan zanga-zangar ɗalibai a jamhuriyar Nijar

    10/02/2026 Duração: 09min

    Ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda ake juyayin cika shekaru  36 da jami’an tsaro suka buɗe wuta kan ɗalibai da ke zanga-zangar neman kyautata ilimi, yin fatali da tsare-tsare Asusun Lamuni na Duniya da sauran matakai na tsuke bakin aljihun gwamnatia jamhuriyar Nijar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla ɗalibai uku. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Yusuf.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan matakin IPOB dakatar da zaman gida na tilas duk Litinin

    09/02/2026 Duração: 09min

    Ƙungiyar ƴan awaren IPOB, da ke fafutukar kafa ƙasar Biafra ta sanar da janye matakin tilastawa jama’a zaman gida a kowace litinin da aka shafe shekaru biyar ana yi a yankin kudu maso gabashin Najeriya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Yusuf don jin cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan kyautar Grammy da Fela Kuti ya samu bayan rasuwarsa

    03/02/2026 Duração: 10min

    Shekaru 29 bayan mutuwarsa, an bai wa shahararren mawaƙi kuma mai fafutuka Fela Kuti ya kasance ba’Afirke na farko da aka bai wa kyautar yabo ta Grammy wato Lifetime Achievement Award da ake bai wa wanda ya sadaukar da rayuwarsa yana rera waƙa. Fela ɗan Najeriya, ya yi fice ainun, ta hanyar rera waƙoƙin gwagwarmaya da kuma muradun talakawa. Shin ko me za ku iya tunawa a game Fela Kuti? Me za ku ce a game da wannan kyauta ta Grammy Awarda aka bayar bayan rasuwarsa? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabambanta

    16/01/2026 Duração: 10min

    Yau  juma'a, rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tattalin arziƙin, siyasa, zamantakewa da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabambanta...

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda wasan kusa da na ƙarshe ya gudana a AFCON

    15/01/2026 Duração: 09min

    Morocco da Senegal sun yi nasarar kaiwa wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afrika ko kuma AFCON, nasarar da suka samu bayan ita mai masaukin baƙi ta doke Najeriya yayinda Senegal kuma ta doke Masar dukkaninsu a daren jiya Laraba, yayinda ake shirin haɗuwa don doka wasan ƙarshe na gasar tsakanin manyan ƙasashen 2 a ranar Lahadi.   Anya kuwa ƙasashen na Masar da Najeriya sun taka rawar da ta dace gabanin fitar da su daga gasar? Wacce ƙasa kuke ganin za ta kai tsakanin labari wajen lashe kofin a wannan karon? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti don sauraren shirin....

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan kayan aikin soji da Amurka ta bai wa Najeriya

    14/01/2026 Duração: 10min

    Amurka ta sanar wa bai wa Najeriya wasu muhimman kayan aikin soji domin tunkarar ƙalubale na tsaro da ƙasar ke fama da shi. Rundunar Amurka mai kula da nahiyar Afirka wato Africom ce ta sanar da hakan, sama da makonni biyu da Amurka ta ƙaddamar da farmakin farko kan wasu wurare ta bayyana cewa maɓoyar yan ta’addace. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

  • Yadda ɗalibai a wasu yankunan arewacin Najeriya ke zaune a gida saboda rashin tsaro

    12/01/2026 Duração: 10min

    A Najeriya, an koma makaranta bayan kammala hutun ƙarshen shekara, to sai dai yanzu haka akwai ɗimbin yara da ba sa zuwa makaranta saboda matsalar tsaro Mafi yawansu a jihohin Katsina, Neja, Sokoto, Zamfara da dai sauransu. Shin ko meye makomar yaran da ba sa samun damar zuwa makaranta sakamakon wannan matsala ta tsaro? Shin waɗannan matakai suku kamata a ɗauka don tunkarar wannan matsala da ke hana ɗimbin yara damar samun ilimi a wasu sassan Najeriya? Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Faruk Yabo.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta

    09/01/2026 Duração: 10min

    Yau juma'a ce ranar da sashen Hausa na RFI ta cikin shirin Ra'ayoyinku masu sauraro ke baku damar bayyana abubuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya, kama daga sha'anin siyasa, tattalin arziƙi, zamantakewa da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙasashe 8 da za su fafata a Quarter Finals na AFCON

    08/01/2026 Duração: 09min

    A gasar neman kofin Afirka da ke gudana a Morocco, a yanzu dai an tantance ƙasashe 8 da za su fafata da juna a matakin da ake kira Quarter Finals, inda Mali-Sénégal, Masar ta haɗu da Côte d'Ivoire, Kamaru ita da Morocco sai kuma Nigeria da za ta kece reni da Algéria. Waɗannan ƙasashe 8, tun farko su ne ake hasashen cewa za su iya taka gagarumar rawa a gasar. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan miliyoyin ƴan Najeriya da basa amfani da wutar mita

    07/01/2026 Duração: 10min

    Hukumar daidaita farashin wutar lantarki a Najeriya ta ce yanzu haka akwai sama da layuka milyan biyar da jama’a ke amfani da wuta ba tare da an ɗora su a kan mita ba. Wannan ya zo ne daidai lokacin da ake ci gaba da ɗiga ayar tambaya dangane da dalilan da suka sa aka gaza samar da mitocin a wadace. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan dokar harajin Najeriya da za ta fara aiki gobe

    31/12/2025 Duração: 08min

    A Najeriya, gobe alhamis 1 ga watan Janairu, za a fara aiwatar da sabuwar dokar haraji ta ƙasa, a cikin yanayi da dokar ke shan suka saboda dalilai da dama. Yayin da jama’a ke cewa sabon tsarin karɓar haraji na matsayin ƙarin nauyi ne ga al’umma, hakazalika wasu ƴan majalisa sun yi zargin cewa abin da suka amince da shi ya sha bambam da abin da gwamnati ke shirin aiwatarwa. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

página 1 de 2