Informações:
Sinopse
Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Episódios
-
Yadda zamani ke tasiri kan salon magana a tsakanin al'umar Hausawa
27/05/2025 Duração: 10minWannan shiri zai mayar da hankali ne kan yadda zamani ke tasiri akan salon magana ko gagara gwari a tsakanin al'umar hausawa, musamman ma matasa masana da dattawa da suka jiya suka ga yau sun bayyana dalilai da suka sanya irin wannan salo na zance, wanda ke nuna ƙwarewar harshe ke neman ɓacewa a tsakanin al'uma da gudummawar da kowanne ɓangare ke bayarwa wajen disashewar wannan fiƙira ta harshe.
-
Shin wa yafi buwaya da kuma kwarewa a waƙa tsakanin Shata da Rarara
20/05/2025 Duração: 10minShirin al'adun mu na Gado na wannan mako zai Dora kan ci gaban Muhawara a tsakanin Masana kan kwarewar waƙa a tsakanin mawaki Shata da kuma Rarara Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin, tare a Nasiru Sani
-
Muhawwara akan bambamci da kamanceceniya tsakanin Shata da Rarara
13/05/2025 Duração: 09minShirin al’adu na wannan makon ya waiwayi al’adar waƙoƙin Hausa ne da kuma tasirin Mawaƙan da suke rera su waƙoƙin a fannonin rayuwa daban daban. A baya bayan nan aka tafka muhawara tsakanin wasu masana guda biyu na Adabin Hausa wato Dakta Abdul-Shakur Yusuf Ishaq na Jami’ar Jihar Kaduna da kuma Dakta Mu’azu Sa’adu Kudan na Jami’ar Sule Lamiɗo da ke Kafin Hausa a jihar Jigawa, waɗanda suka baje iliminsu a kan matakin shahara, da kamance-ceniya da kuma banbanci a tsakanin Marigayi Mamman Ibrahim Yero da aka fi sani da Mamman Shata ko kuma Shata mai Ganga da kuma Dauda Adamu Kahutu Rarara da a halin yanzu zamani ke tafiya da shi.
-
Yadda camfi ke shafar rayuwar al'umma a wannan lokaci
06/05/2025 Duração: 10minShirin a wannan makon zai tattauna ne a kan Camfi, da kuma yadda ya kasance a zamanin kaka da kakanni, da rawar da ya taka a waccan lokaci da kuma yadda yake shafar rayuwar jama’a a lokacin da muke.Duk da ƙarancin lokaci, shirin Al’adunmu na gado zai yi ƙoƙarin zayyana rabe-raben al’adar ta Camfi ko kuma wasu daga ciki.