Kasuwanci

Najeriya da China sun yi bukin cika shekaru 55 da hulɗar diflomasiyya

Informações:

Sinopse

Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan tasirin tattalin arziki dangane da alaƙar China da Najeriya da a makon jiya aka yi bikin cika shekaru 55 da faro hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu. Najeriya da China sun sake jaddada karfafa dangantakar diflomasiyya da ke tsakaninsu yayin da kasashen biyu ke bikin cika shekaru 55 da fara huldar diflomasiyya a bikin baje kolin sabuwar shekarar kalandar kasar China da aka gudanar.