Wasanni

An kammala gasar kokowa ta ƙasa mafi girma a Jamhuriyyar Nijar

Informações:

Sinopse

Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda aka kammala gasar kokuwar gargajiya ta ƙasa a Jamhuriyar Nijar. Jiya Lahadi ne aka kammala gasar kokowar gargajiya ta ƙasa a Jamhuriyar Nijar da aka gudanar a garin Tawa, wacce ita ce karo ta 46, inda mai masaukin baki ta lashe takobin bayan ƴan kokowarta biyu sun kai wasan ƙarshe a wannan gasa. Bayan karawa ta mintuna 11 da daƙiƙu 6, Nura Hassan ne ya yi nasara kan Zakiru Zakari. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.