Al'adun Gargajiya

Yadda aka gudanar da bikin naɗin sarautar sarkin Komadugu a Maraɗi

Informações:

Sinopse

Shirin na yau ya yada zango jihar Diffa dake Jamhuriyar Nijar,yankin da aka gudanar da bikin nadin sabon sarkin Komadugu, wanda ya samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar. Diffa dai kamar dai yadda masana tarihi suka tabbatar, ana na nufin Diwa a harshen Kanuri kenan. Kalmar ta samo asali ne daga kalmar "Di wa Nallé wa," wadda ke nuna tsabtar jiki da dai sauran abubuwan da suka shafi maza da mata na yankin. Di na nufin farin gashi, kuma Nallé na nufin lalle wanda ke da ma'ana biyu. Wannan jumla, Di wa Nallé wa, na nufin mata waɗanda, ko da a cikin tsufa, suna rina gashinsu da lalle. Tarihi ya nuna  cewa a ƙarni na 19, yankin Diffa a lokaci na karkashin masarautar Kanem-Bornu,inda a shekarar 1933 Turawan mulkin mallaka a lokacin  sun kafa yankin Komadougou, wanda aka bayyana yankin  da farko yake zaune a Bosso sannan daga baya ya koma Gueskérou. An gudanar da zaɓen sabon sarkin na komadugu a jahar Diffa a gaban hukumomin  bariki da na gargajiya da kuma sauran al’umma, wanda ya kai ga zaɓen Hassan Mamadou A