Wasanni
Matsalar da hukuncin ɗauke wasan Kano Pillars da Katsina Utd a gida ya ja musu
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editora: Podcast
- Duração: 0:10:03
- Mais informações
Informações:
Sinopse
Shirin awannan mako zai duba batun hukuncin ɗauke ƙungiyoyin Kano Pillars da Katsina United daga buga wasannin sun a gida a gasar NPFL ta Najeriya, da hukumar da ke shirya gasar ta yi. Kamar yadda masu bibiyar gasar Firimiyar Najeriya suka sani ne a baya bayannan, Hukumar Shirya Gasar NPFL ta Najeriya ta ɗauki hukuncin dakatar da manyan ƙungiyoyin arewacin Najeriya biyu wato Kano Pillars da Katsina United daga buga wasannin su na gida, inda aka maida Pillars buga wasan ta a Jihar Katsina, yayin da ita kuma Katsina United aka mayar da ita buga wasannin ta a jihar Pilato.