Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun yi watsi da sabon harajin da CBN ya bullo da shi

Informações:

Sinopse

Ƙungiyar Ƙwadago da sauran kungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi fatali da matakin gwamnati na baiwa bankuna umarnin fara cirar harajin kashi 0.5 wato rabin ɗaya kenan cikin 100, kan duk hada-hadar aika kudaden da ‘yan kasar ke yi ta intanet. A cewar gwamnatin za a rika amfani da sabon harajin don samar da tsaro daga barazanar masu yi wa mutane kutsen satar kuɗaɗe da sauran muhimman bayanai ta shafukan intanet.Sai dai ƙungiyoyin sun ce sabon harajin zai sake jefa ‘yan Najeriya musamman matsakaita da masu ƙaramin ƙarfi ne cikin ƙarin ƙunci, bayan matsin da suke ciki.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.